<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>297</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya ƙaunar Almasihu,
 Ban san iyaka ba,
 Da zurfinta da tsawonta
 Sun wuce faɗina.
 A gindin giciyen Almasihu
 Na zauna, hutun rai na yi.
 Rijiyar ƙauna cikakkiya da rai,
 Kai ka bayar a shayad da ni.

[V2]
 2) Ya ƙaunar Almasihu
 Wadda ta riƙe ni,
 Ta bi ni, ina nesa,
 Ta kawo ni wurinka.
 Ta amshi dukan zuciyata,
 Ta sa na zama bawanka.
 Duniya duk ta kasa jawo ni,
 Domin ikon ƙaunarka.

[V3]
 3) Ya ƙaunar Ubangiji,
 Ya zuciyar Allahnmu,
 Ga zunubi a duniya,
 Ga girman ƙaunarka.
 Ga ƙofar rai a buɗe yau,
 Ƙauna ta buɗe ta.
 Ba mu yin fahariyar kome,
 Sai dai giciyen Almasihu.</lyrics>
<title>Ya Ƙaunar Almasihu, Ban San Iyaka Ba LW297</title>
</song>